JARUMI kuma babban furodusa Malam Dan'azimi Baba Cediyar Yangurasa ( wanda aka fi sani da Kamaye ) ya karyata labarin da ake yadawa cewa wai ya rasu . Tun a safiyar yau alhamis dai aka tashi da yaduwar labarin , aka shafe tsawon wuni ana baza shi a soshiyal midiya , har ta kai wasu su ka dauka gaskiya ne , su na buga fosta da rubutun Allah ya jikan shi .
Amma jarumin na cikin shirin ' Dadin Kowa ' ya yi magana da Duniyar Kannywood kan labarin , ya ce : " To , ni dai haka na ga labarin a soshiyal midiya , kuma daga baya ake ta bugo mini waya ana cewa na mutu . Ni dai a yanzu ina nan da rai na , ban mutu ba . Kuma lafiya na ke , ina ci gaba da harkokin da na ke yi . "
