Yayin da dala ke daf da kaiwa naira dubu guda

Yayin da dala ke daf da kaiwa naira dubu guda

 A halin yanzu hukumar yaki da masuyiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a naJeriya wato EFCC , ta kama yan canji 87 a babn birnin taraiya dake abuja dakuma jahohin lagos da kano acigaba da kawo karshen matsalar  karanci da tashin farashin dala da ake fuskanta a kasar.

Jaridar punch tarawaito cewa jamian hukumar EFCC tayi dirar mikiya a wasu dagacikin wuraren canji kudi dake abuja tare da kama mutane 25 masu gudanar da harkar ta haram tacciyar hanya Wanda yake zuwa bayan kama wasu 40, adadin daya nuna cewa mutane 65 kenan hukumar ta kama a abuja. 

Hakanan jamian hukumar sun kama wasu yan canji 14 a jihar lagos dakuma mutum 8 a kasuwan canjin kudi a wapa dake ji

har kano.

Duk dayake babu wasu Dalilan game da kame da hukumar EFCC ta bayar, amma ana ganin hakan yana da alaka da kokarin bin didigin asalin kudaden da ake tunanin yan taadda da kuma wasu yan siyasan Kasar zasu fiddo don sauyasu zuwa kudaden ketare game da ummarnin babban bankin kasa wato CBN na sauya  fasalin wasu takardun kudin kasar a watan gobe.

 AHALIN DA AKE CIKI:-

Dalar amurka zata iya zarta naira dubu 1 kowani lokaci daga yanzu domin anfara saidata dubu guda a wasu wurare a kasar.

Saidai yan canji sun meyar da martani, idan sukace tsare-tsaren gwamnatin Buhari na kokarin canja kudin kasarne ya jefa kasar cikin halin da take ciki.

Post a Comment

Previous Post Next Post