Binciken da akayi an gano cewa Rahama Saleh Ahmed ( Ummi Rahab ) , wato matar mawaki , furodusa kuma jarumi Shu'aibu Ahmed Abbas ( Lilin Baba ) , wadda kuma tsohuwar jarumar Kannywood ce , ta bayyana cewa ta samu ciki.
A shafin , an wallafa sako da Turanci da manyan bakake : " I'm pregnant " , wanda aka fassara da , " Na samu ciki " . Dimbin masu bibiyar shafin a Instagram wadanda ke tunanin Ummi Rahab ce sun tura sakonnin taya ta murna tare da yi mata fatan alheri.
