Bayan Da jami'an tsaro suka kame wannan ma'abocin dandalin Facebook din mai suna Indabawa Aliyu Imam bisa Zargin bata suna ga Abdul Saheer da Aka fi sani da Malam Alk a shirin kwana chasa'in Indabawa ya amsa laifin sa cikin nadama da dana sani inda ya bayyana sharrin zuciya da zafin kai ne ya kai shi ga aikata wannan abu.
Kakakin hukumar yan sandan Jahar Kano Abdullahi haruna kiywa ne ya bayyana hakan bayan da suka zanta da Indabawan kan dalilin sa na aikata wannan danyan aiki inda akarshe ya nemi Afuwar Malam Ali da kuma jan hankali ga masu tunni irin nashi